Shugaban kasa, Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kudin 2024 ga majalisar dokokin kasarnan a cikin watan Nuwamba dake tafe.
Ana kuma saran shugaban kasar ya mika kwarya-kwaryan kasafin kudin shekarar 2023 ga majalisar dokokin kasarnan domin nazari da tantancewa da kuma amincewa.
Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa, Solomon Adeola, wanda ya bayyana hakan a yayin taron kaddamar da kwamitin a ranar Laraba, ya bayyana cewa majalisar za ta tabbatar da cewa an zartar da kasafin kudin 2024 akan lokacin da ya dace.
Hakan na zuwa ne lokacin da Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu, ya ce Najeriya ta zama dandali na masu zuba jari daga kasashen waje don cin gajiyar abubuwa da dama.
Ministan ya bayyana haka ne a karshen taron tattalin arzikin Najeriya na 2023 a Abuja.
Bagudu ya ce duk da kalubalen da kasarnan ke fuskanta, gwamnati ta ci gaba da jajircewa, kuma tana ci gaba da gudanar da ayyukan tattalin arziki a dukkan sassan kasarnan.