Mutanen biyu da ake kallon basa ga maciji da juna sun Yi ganawar Sirri ne a Ranar Laraba.
Mutanen biyu sun rufe kofa a yau Laraba Yayin wata ziyara ta musamman da Bola Ahmed Tinubu Ya Kai gidan tsohon shugaban kasa dake Abeokutan jihar Ogun.
Duk da cewar Babu cikakken labarin abunda ganawar ta kunsa a yanzu, sai dai wasu rahotanni na baiyana cewa bata rasa nasaba da zaben shugaban kasa mai zuwa, Wanda Tinubu ke yiwa APC takara.
Tinubu ya samu rakiyar wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC, kamar kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabimiala da Gwamnan jihar Dapo Abiodun da Sauran masu fada aji na Jam'iyyar.
Ganawar tasu tazo ne Yan kwanaki bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakunci Tinubu da Kashim Shatima da Kuma Babban Daraktan Yakin Neman zabensa, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato a fadarsa dake Villa Abuja.
Ku cigaba da kasancewa damu a shafin nan, domin kawo maku yadda ta wakana.