Rahotanni na baiyana cewar, Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kammala shirin hada tsohon gwamnan jihar AkwaIbom, Sanata Godswill Akpabio, da Sanata Jibrin Barau daga nan kano a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa
Akpabio da Barau na daga cikin ‘yan takara 9 da za su fafata a zaben shugabancin majalisar dattijai da ake sa ran za a kaddamar a ranar 13 ga watan Yuni.
Majiya mai tushe ta shaida wa jaridar Daily trust cewa zababben shugaban kasar wanda ya dawo kasar nan a ranar Litinin bayan ya kwashe kwanaki 34 a kasar waje, ya bayyana sha’awarsa ta tsayar da Akpabio da Barau a matsayin wanda zasu jagoranci majalisar dattawa a yayin wani taro da aka yi a Abuja.
A ranar Talata ne tsohon gwamnan jihar Legas ya gana da Sanata Akpabio da Sanata Barau sai kuma Sanata Opeyemi Bamidele na jihar Ekiti da kuma gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji.
Majiyoyi sun ce, a yayin taron, An bukaci Barau ya janye kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin majalisar dattawa domin samun hadin kan kasa da kuma daidaito.