On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Tinubu Ya Wajabta 'Daukarwa 'Kasa Alkawari Bayan Rera Taken Najeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin wajabta rera alkawarin 'kasa bayan taken Najeriya a duk wani taro na gwamnati da jama'a.

Hakan wani mataki ne na tabbatar da cikakkiyar mutuntawa  ga 'kasa da karfafa biyayya  ga dokokin kasa da kuma kiyaye martabar Najeriya da kishinta.
 
Da yake jawabi a wajen kaddamar da ginin rukunin gidaje  na Renewed Hope City a yankin Karsana dake Abuja, a ranar Alhamis, shugaban ya jaddada wajibcin mutunta kimar kasa da  inganta manufofin kasa da biyayya ga dokokin da aka kafa.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Chief Ajuri Ngelale ya fitar, 
Tinubu ya ce  kafin ya bar gida a safiyar yau (Alhamis)  ya umarci a buga takardar rubutun alkawarin kasa, kuma dole ne a sake farfado da shi daga taron na yau (Alhamis). 

"Mun gani a filin wasa jiya, muna murna, kowa yana son nasara, muna son cin nasara.” in ji Shugaba Tinubu.