kuma, kakakin shugaban kasa Ajuri Ngelale ,Ya ce shugaban kasa Bola Tinubu, Bai damu da yadda zata kaya a hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa zata yanke a gobe ba.
A hirarsa da gidan Talabijin na Channels a daren jiya, Y ace shugaban kasar baya kallon wata barazana dangane da hukuncin kotun.
Haka zalika ya ce shugaban kasar nada kwarin gwiwa akan hukuncin da kotun zata yanke, la’akari da kwararran hujjojin da bangarensa ya gabatar.
Bugu da kari ya ce shugaban kasar nada kwarin gwiwa ga bangaren shari’a, wanda ya ce yana da yakinin za’a sake tabbatar masa da nasararsa da ya samu.