Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tare da jam’iyyar PDP sun shiga tsakani domin ganin sun dakile yunkurin tsige gwamnan jihar Ribas Sim Fubara.
Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta yi maraba da matakin shiga tsakani da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi akan rikicin siyasar jihar Ribas, inda ya yi kira ga bangarorin da takun saka da juna, dasu maida wukar cikin kubenta.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da gwamnonin suka fitar a yammacin jiya Talata bayan sun gana a masaukin gwamnan jihar Oyo da ke Abuja inda suka tattauna kan rikicin siyasar jihar Ribas mai arzikin man fetur da sauran wasu batutuwan da suka shafi kasa.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana cewa Gwamnonin PDP sun damu da irin abubuwan dake faruwa a jihar Ribas, kuma sun yi maraba da matakin sasanta rikicin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi.
Taron ya bukaci dukkan bangarorin da ke rikici da juna a jihar Ribas da su yi amfani da hanyoyin masalaha wajen warware rikicin cikin lumana.
Taron gwamnonin na PDP a jiya Talata, ya biyo bayan rikicin siyasar da barke a jihar, wanda ta kaiga majalisar dokokin jihar ta yi yunkurin tsige Gwamna Sim Fubara, daga kan kujerarsa.