On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Tinubu Ya Rubuta Wasikar Neman Amincewar Majalissa Domin Tura Sojoji Jamhuriyar Nijar

Shugaba Bola Tinubu ya rubutawa majalisar dattawa wasika yana neman a tabbatar da matakin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta yanke kan halin da ake ciki a jamhuriyar Nijar.

A cikin wasikar da aka karanta a zauren majalisar dattijai, Tinubu ya yi nuni da cewa, biyo bayan yanayin siyasar jamhuriyar Nijar da ya kai ga hambarar da shugabanta, kungiyar ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulkin baki daya tare da kuduri aniyar neman dawo da gwamnatin da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.

Ya kuma kara da cewa, a wani yunkuri na maido da zaman lafiya, kungiyar ECOWAS a cikin wata sanarwar da ta fitar ta kuduri aniyar rufewa tare da sanya ido kan iyakokin kasa da kasa na  jamhuriyar Nijar tare da katse wutar lantarki ga kasar. 

Sauran shawarwarin sun hada da tara tallafin kasashen duniya don aiwatar da tanade-tanaden sanarwar kungiyar ECOWAS ta kuma yi kira da a hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci da na musamman a ciki da wajen Jamhuriyar Nijar.

 Ya hada da hana kayayyakin da ake jigilarsu zuwa Nijar musamman daga Legas da tashar jiragen ruwa ta gabas da kuma fara wayar da kan 'yan Najeriya da 'yan Nijar  kan wajibcin wadannan matakai musamman ta kafafen sada zumunta. 

A karshe shugaban ya bukaci ‘yan majalisar da su duba bukatar tura Sojoji domin tilasta bin tsarin mulki ga sojoji a Nijar idan har suka bijire.