On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Tinubu Ya Nada Sabbin Kwamishinonin INEC 9

Bisa ikon da sashe na 154 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya da sashe na 6 na dokar zabe suka tanada, shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin kwamishinonin zabe na jahohi tara, a hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC.

A cikin wani sabon jerin sunaye da aka bayyana a ranar Laraba ta hannun mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya lissafa sabbin kwamishinonin da suka hadar da Isah Ehimeakne na jihar Edo sai  Mrs. Oluwatoyin Babalola a Ekiti da Abubakar Ahmed Ma'aji a Gombe da kuma Shehu Wahab a Kwara.

Sauran sun hada da Dr. Bunmi Omosheyindemi a Lagos sai Aminu Kasimu Idris a Nasarawa da Farfesa Mohammed Yalw na Neja da Dr. Anugbum Onuoha, a jihar Rivers da kuma  Isma'ila Kaura Moyi a jihar Zamfara.

Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin kwamishinonin zaben  da su kasance masu bin ka’idoji da kwarewa da da’a wajen gudanar da ayyukansu, ta yadda za su dora wani sabon tsari mai dorewa da gudanar da zabe ba tare da rikici ba a Najeriya.