Shugaban kasa Bola Tinubu, Ya taya daukacin al’ummar Musulmi a kasar nan da ma duniya baki daya, murnar sake zagayowar bukukuwan babbar Sallah, Tare da yin kira ga al’ummar Musulmi da su kasance masu yin godiya ga Allah madaukakin sarki da ya ba su damar sake ganin lokacin.
Shugaban taraiyyar Najeriyar ya sauka filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas bayan da ya taso daga birnin Landan da misalin karfe 5 da mintina 13 na yammacin jiya.
A sakonsa na barka da Sallah, Shugaban kasar ya yabawa ‘yan Najeriya bisa hakuri da kuma juriya da suke nunawa da yanayin tsadar rayuwa da ake ciki.
Kazalika ya ce yana sane da irin kalubalen da jama’a da jama’a ke ciki, sai dai kuma shi da masu dafa masa baya, suna yin aiki tukuru, domin ganin an magance matsalolin ta yadda al’umma zasu amfana.
A cewarsa, yayin da ‘yan Najeriya ke nuna juriyarsu da tsadar rayuwa da ake ciki, dole ne suma makomarsu ta kasance mai farin ciki, ta yadda goben yan Najeriya zata kasance san barka fiye da yadda ake ciki a yanzu.