Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar ‘yan wasan Najeriya ta Super Eagles murnar nasarar da suka samu akan kasar Afrika ta Kudu, a wasan kusa da na karshe na gasar cin Kofin nahiyar Afrika da suka buga a daren jiya.
Super Eagles ta doke kungiyar kwallon kafa ta Bafana-Bafana da ci 4 da 2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, Bayan tashi wasan ana ci 1 da 1, duk da karin lokacin da aka yi, a wasan da suka buga a kasar Coted’Ivoire.
Dan wasa Kelechi Iheanacho ne ya ci kwallo ta karshe a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da mai tsaron gidan Najeriya Stanley Nwabali ya tare kwallaye biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga, wanda hakan yasa Najeriya ta kai wasan karshe na gasar.
Da yake tsokaci kan nasarar da kungiyar ta samu a shafinsa na X, Shugaban kasa Tinubu ya jinjinawa kungiyar ta Super Eagles saboda nasarar da suka samu, tare da kara jan hankalinsu akan su jajirce domin ganin sun samu nasara a wasan karshe na gasar.