To a wani mataki na gaggawa da aka dauka domin shawo kan matsalar ta Man fetir, Shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da shugaban kanfanin mai na kasa NNPC, Mele Kyari da gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele da sauran manyan mukarraban gamnati a fadar shugaban kasa a ranar Talata.
Kyari ya fadawa manema labarai bayan taron cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta iya cigaba da biyan tallafin mai ba, inda ya kara da cewa kamfanin na bin gwamnatin taraiya bashin Naira tiriliyan 2 da bilyan 8 da aka yi amfani dasu wajen biyan tallafin mai a Kasar nan.
Da yake tabbatar da matsayar shugaban kasar, Mele Kyari ya tabbatar da cewar, gwamnati ba zata iya cigaba da biyaan tallafin man ba, saboda yana wahalar da kamfanin wajen samar da kudin da za’a yi amfani dasu wajen biyan tallafin.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnati za ta fara daukar matakan dakile illolin cire tallafin ba tare da bata lokaci ba.