A jiya ne shugaban kasa Bola Tinubu ya karbi bakuncin shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz a fadar mulkinsa da ke Abuja
Wannan ce ziyarar farko da Shugaban gwamnatin Jamus ya taba kawowa Najeriya a karon farko tun bayan hawansa karagar mulki a watan Disambar 2021.
Shugabannin biyu sun amince da karfafa huldar dake tsakanin kasashen biyu ta bangaren tattalin arziki da kuma amfani da ma'adanan da kasar nan ke dasu .
Shugaba Tinubu ya ce shirinsa na farfado da tattalin arzikin kasa ya fara haifar da samun ‘Da mai ido ga bangaren zuba jari a kasar nan.
Shima a nasa jawabin shugaban gwamnatin jamus Olaf Scholz ya ce kasarsa ta Jamus za ta kara yin nazari kan harkokin kasuwanci a Najeriya, tare da mutunta tsarin dimukuradiyya da kuma yin aiki da doka.