Fadar shugaban kasa ta baiyana cewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wanda ke zama shugaban kungiyar ECOWAS, bai yanke hukuncin daukar matakin soja akan jamhuriyar Nijar ba, Sai dai yayi amannar cewar yin amfani da matakan Diflomasiyya shi ne mafita wajen warware rikicin da kasar ta samu kanta a ciki.
Wannan sanarwa na zuwa ne a yayin da a jiya,Kungiyar ta ECOWAS ta sake amincewa da ‘ka’kaba sabon takunkumi akan daidaikun mutane dake hulda da sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar.
Sai dai sanarwar da kakakin shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya fitar, ta jaddada cewar shugaban kasa Tinubu da sauran shugabannin kasashen Afrika, sunfi son yin amfani da Diflomasiyya wajen warware takaddamar.
Ya kuma ce wa’adin kwanaki bakwai da aka baiwa sojojin da suka yi juyin mulki, ba matsayar da shugaban kasa Bola Tinubu ya dauka ba ce, Illa dai mataki da kungiyar ta ECOWAS ta dauka.