Dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Ya ce ya gano wata makarkashiya da ake kullawa domin kawo rudani, wanda zai haddasa dage lokacin gudanar da zaben shugaban kasa da za’a yi ranar 25 ga watan da muke ciki.
Ya yi wannan zargin ne a yayin gangamin yakin neman zabensa da aka gudanar a birnin Ado Ekiti na jihar Ekiti a ranar juma’a.
Tinubu ya ce aniyar wasu mutane na kawo tazgaro wajen gudanar da zaben nada manufar ganin an kafa gwamnatin rikon kwarya, sai dai kuma ya ce shirin nasu ba zai samu nasara ba.
Tsohon gwamnan na Legas, ya bukaci jama’ar kasa da suyi tsayuwar daka tare da kaucewa yin duk wani abu da zai haddasa tashin zauni tsaye, da kuma tabbatar da cewar suna da katin zabe .
Kalaman Tinubu na zuwa mako daya, Bayan da yayi zargin cewar ana shirin kawo wargaza zabe mai zuwa, ta hanyar amfani da karancin man fetir da kuma sauya fasalin takardun Naira.