Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya musanta rade-radin da ake yi na cewar zai mayar da jihar Legas, babban birnin taraiyyar kasar nan, a maimakon Abuja, idan har aka zabe shi a kan matsayin shugaban kasa.
Ta cikin wata sanarwa da Majalisar yakin neman zaben shugaban kasa ta jam’iyyar APC, ta fitar, Ta karya jita-jitar tare da yin Allah wadai da ‘yan Hamaiyya kan salonsu na bata suna a lokacin yakin neman zabe, da kuma ta’ba muhibbar dan takararsu na shugaban kasa.
Sanarwar mai dauke dasa hannun daraktan yada labarai da wayar da kai na majalisar yakin neman zaben, Bayo Onanuga, Ya ce Tinubu bashi da irin wannan shiri kuma ba zai yi duk wani abu da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa ba.