Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, Yace Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu Ya amince ya Zabi Musulmi a matsayin wanda zai yi masa takarar mataimaki.
Ya tabbatar da haka ne a ranar Juma’a, yayin wani taron addu’a na musamman da aka shirya wanda malamai 100 suka halarta a fadar gwamnatin jihar Kano. Gwamnan yace an bawa tinubu shawarar daukar musulmi a matsayin mataimakinsa, kuma ya amince da hakan.
Yace tsarin bayar da tikitin takarar shugaban kasa dana mataimakinsa ga musulmi kadai ba wani sabon al’amari ba ne a kasar nan, A bisa haka ne yayi kira ga malaman da su yiwa addu’ar zama shugaban kasa a zabe mai zuwa.