Adadin wadanda suka mutu sakamakon gobarar tankar mai a wata mahadar titi dake garin Dikko kusa da Suleja a jihar Neja ya karu zuwa 86, yayin da mutane 55 suka samu raunuka, inda suke samun kulawar gaggawa a asibiti.
A ranar Asabar da lamarin ya faru, adadin wadanda suka mutu ya kai 70 sannan guda 50 suka jikkata. Sai dai kuma an kara gano karin gawarwaki tare da yi musu jana’iza a garin na Dikko.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago, wanda ya ziyarci wurin da gobarar tankar man ta faru, ya hana ababen hawa da suke tahowa daga yankin Maje wucewa ta gadar Dikko.
Shima a nasa bangaren, shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana matukar alhininsa kan ibtila’in da ya faru, sannan kuma ya umarci hukumomi da abun ya shafa da su bayar da cikakkiyar kulawa ga wadanda suka samu ‘kuna, tare da umartar hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa data tabbatar ta dauki matakan kare afkuwar irin hakan a nan gaba.