Shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da masu taimaka musu a fadar shugaban kasa, za su kashe kudi naira biliyan 15.961 wajen tafiye-tafiyen kasashen waje da na cikin gida a shekarar 2024.
Wannan adadi yana kunshe ne a cikin kudirin kasafin kudin shekarar 2024, wanda yanzu haka majalisar dokokin kasar ke nazari akai. .
Bayanin adadin ya nuna cewa shugaba Tinubu zai kashe zunzurutun kudi har Naira billiyan 7 da milliyan 630 na tafiye-tafiye, wanda ya kasance mafi yawan kudaden da za a kashe a tafiye-tafiyen kasashen waje.
Idan majalisar tarayya ta amince, zai kashe Naira biliyan 6.992 wajen tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da kuma Naira miliyan 638.535 wajen tafiye-tafiye a cikin kasarnan.
Hakazalika, mataimakin shugaban kasa Shettima zai kashe jimillar Naira biliyan 1.847 a balaguron kasa da kasa.
A tsarin kasafin kudin, zai kashe Naira biliyan 1.229 wajen tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da kuma Naira miliyan 618.399 a tafiye-tafiyen cikin gida.