Kotun Kolin ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar suka daukaka a gabanta dake neman a soke cancantar takarar Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shattima na jam'iyyar APC.
A hukuncin da kotun mai alkalai biyar ta sanar a yau Juma'a ta ce jam’iyyar PDP ba ta da dama a doka ta yi kara akan al’amarin saboda acewar kotun PDP ba tad a hurumi a jam'iyyar APC.
Masu karar suna ikirarin cewa zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu ya saba wa sassa na 29 (1) da 33 da 35 da kuma na 84 (1) (2) na dokar zabe ta 2022.
A karar sun ce Shettima ya sabawa dokar saboda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa da kuma kujerar majalisar dattawa ta Borno ta tsakiya a lokaci daya.
Saboda haka ne wadanda suka shigar da karar suke neman kotun ta soke cancantar takarar APC da Tinubu da Kashin Shettima.