A yayin da ake ci gaba da mayar da martani kan tsoma bakin shugaba Bola Tinubu kan rikicin da ya dabaibaye jihar Rivers, lauyan kare hakkin bil’adama, Femi Falana, ya ce shugaban kasar ba zai iya mayar da ‘yan majalisar dokokin jihar su 27 da ke fuskantar takaddamar Sauya she'ka ba.
A cikin wata sanarwa a ranar Talata, Falana, babban lauyan Najeriya mai kwarewar SAN, ya ce tilas ne a ko da yaushe tsoma bakin shugaban kasa ya kasance bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa.
A cewarsa, tuni aka ayyana kujerun ‘yan majalissar a matsayin wadanda babu kowa kamar yadda doka ta yi tanadi.
Har ila yau, ya zama wajibi INEC ta gudanar da zaben da zarar an soke umarnin da babbar kotun tarayya ta bayar a ranar Juma’ar da ta gabata.
Ya ce ‘yan majalisar da ke rike da madafun iko za su iya rike kujerunsu ne kawai idan sun tabbatar da cewa jam’iyyar siyasar da suka ci zabe a karkashinta d ta rabu gida biyu ko fiye da haka.