Wani jirgin kanfanin Max Air da ya taso daga birnin Yolan jihar Adamawa a ranar Lahadi yayi gaggawar sauka,wanda hakan yayi sanadin soke tashin jiragen sama da dama da kuma jinkir ta tashin wasu.
Mafi akasarin jiragen da abun ya shafa sune wadanda basa sauka idan dare ya yi, A yayin da kanfanin jirgin sama na Air Peace ya sanar da soke tashin jiragensa da dama, kamar yadda ya aike da sakon kar ta kwana ga Fasinjojinsa.
Kazalika sauran wasu kanfanonin sun soke tashin jiragensu, lamarin da ya sa matafiya da dama suka makale a filin jirgin saman Abuja.
Saukar gaggawar da jirgin ya yi, tasa an dan rufe titin da ya sauka na dan wani lokaci a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, Kafin jami’an bada agajin gagagwa su kaiga dauke jirgin sannan kuma aka gyara wajen da abun ya faru.
Rahotanni sun baiyana cewar tayar jirgin ce ta fashe a daidai lokacin da jirgin ke kokarin sauka, Lamarin da ya sashi yin saukar ba zata, amma ba’a samu asarar rai ba.
Mai magana da yawun hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa,Uwargida Faithful Hope Ivbaze, ta tabbatar da janye jirgin daga wajen da ya sauka da karfe 8 da kwata na dare, a yayin da yanzu haka aka fara yin bincike.