Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa ASUU ta ce batun sake tattaunawa kan yarjejeniyar shekarar 2009 tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar ya kai wani mataki na cigaba mai ma’ana.
Ƙungiyar ta ƙarfafa membobinta su ci gaba da mai da hankali har zuwa ƙarshen abunda ya turewa buzu Nadi..
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata wasika da shugaban kungiyar na kasa Farfesa Emmanuel Osodeke ya sanya wa hannu, kuma ta mika wa dukkanin sassan kungiyar da manema labarai suka samu kwafi a ranar Lahadi.
Osodeke, a cikin sanarwar, ya bayyana cewa, kungiyar ta gudanar da taro sau biyar tare da wakilan gwamnatin tarayya, yayin da ta yi ganawa biyu da ministan ilimi, Adamu Adamu.