On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Talauci Da Rashin Ilimi Da Kuma Tashe-Tashen Hankula Sun Zama Tarnaki Ga Mata A Najeriya - ActionAid

Mataimakiyar darakta kungiyar ActionAid Najeriya, Hajiya Suwaiba Muhammad 'Dankabo, ta ce da tallafin GCERF karkashin shirin yaki da tsatsauran ra'ayi SERVE III, da shirin sasanta rikice-rikice da samar da cigaba DRDI-DAG, sun mika kayayyakin sana'o'i na sama da Naira miliyan 40 ga Mata da Matasa 300 da aka horar kan sana'o'in dogaro da kai a Jihar Kano.

Hajiya Dankabo, ta bayyana haka ta taron bikin ranar Mata ta duniya da aka gudanar a dakin taro na Sani Abacha, ta kara da cewa rashin ilimi da talauci da tsoron tashe-tashen hankula da rashin jari na daga cikin ƙalubalen da Mata ke fuskanta a wannan lokaci, inda ta bayyana samar kyawawan manufofi daga gwamnati sune zasu karfafa Mata. 

Da yake zantawa da wakilin mu Kamaluddeen Mohammed, babban daraktan, cibiyar sasanta rikice-rikice da samar da cigaba, Dr Muhammad Mustapha Yahaya, yace taken taron na bana shine " zuba jari don samarwa Mata cigaba" wanda hakan ne nufin ingantaccen ilimin su da haɓaka harkokinsu na Yau da gobe da basu damar da ta dace.

Dr Mustapha, ya kara da cewa a bana za'a horar da Mata da masu ruwa da tsaki 1000 hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya da hakuri da juna, yana mai cewa za su cigaba da samar da hanyoyin ƙare Mata da Yara daga duk wani nau'in cin zarafi ta hanyar ƙarfafa tattalin arzikin su da damarmaki na a dama dasu harma da yancin su kasancewar addinin Musulunci ya daɗe da tsare musu ire-iren waɗannan haƙƙoƙi nasu.