Naira Dari 4 da 16 da Kobo 62 a ranar Talata
An canzar da takardar kudi ta naira kan 416 da kobo 62 akan kowace Dala 1 a ranar Talata a kasuwannin ‘Yan canji, wanda hakan ya nuna cewa takardar nairar ta ‘dan samu tagomashin kobo 9 akan kowace Dala 1 idan aka kwatanta da yadda aka yi musayarta Ranar Litinin, akan naira 417 kan kowace Dala guda.
Rahotanni sun baiyana cewa Darajar takardar Dalar sai da ta kai har naira Dari 4 da 44 kafin daga bisani ta sauka zuwa Naira Dari 4 da 16 da Kobo 62 a ranar Talata.
Gabaki daya jimillar kudaden musayar da aka yi canjinsu a ranar Talata kadai, ya kai Dala Milyan 127 da Da dubu 12.