Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta kasa, Amaju Pinnick, Ya yaba da kwazon da tawagar yan wasa mata ta kasa, Super Falcons suka nuna, bayan nasarar da suka samu ta tikitin shigar gasar cin kofin kwallon kafar mata ta duniya ta shekarar 2023.
Kungiyar Super Falcons ta doke kungiyar Indomitable Lionesses ta kasar Cameroo da ci 1 tak mai ban haushi a wasan kusa dana karshe da suka yi a daren jiya, a cigaba da buga wasan cin kofin nahiyar afrika na mata da ake yi a kasar Moroco.
Najeriya wadda ta dauki kofin gasar har sau 9 na fatan ganin a wannan karon ma ta daga kofin gasar a karo na 10 a kasar Morocco.