Babban sufeton yansanda na kasa Kayode Egbetokun, ya nuna rashin amincewarsa da kirkirar ‘yan sandan jihohi, inda ya yi gargadin cewar gwamnonin jihohi zasu mayar dasu yan amshin shata, ta hanyar hada baki da su domin tauye hakkin wani ko kuma bullo da wata matsala ta tsaro.
Sufeton yansandan ya baiyana haka a yayin wani taro da majalisar wakilai ta shirya domin yin muhawara kan samar da yansandan jihohi a jiya.
To sai dai kuma gwamnatin tarayya ta sake jaddada cewa babu ja da baya kan shirin samar da yansandan jihohin.
A yayin taron mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya nanata kudirin gwamantin shugaban kasa Bola Tinubu na samar da kyakykyawan tsari wajen kirkirar yansandan jihohin.