On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Sojojin Nijar Sun Gargadi ECOWAS Kan Amfani Da Karfi Wajen Dawo Da Mulkin Farar Hula

Shugabannin  Sojin da suka yi  juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun gargadi shugabannin kungiyar kasashen ECOWAS da su kauce wa duk wani shiri na tura sojoji kasarsu da zummar mayar da tsohuwar gwamnatin da suka kawar daga karagar mulki. 

Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijar, Janar Abdourahmane ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa, inda Mohamed Bazoum ke hannun sojoji tun bayan juyin mulkin da aka yi a makon jiya.

A karshe kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin shugaba Tinubu ta ba da wa'adin kwanaki bakwai ga gwamnatin mulkin soja a Nijar da ta maida shugaba Bazoum kan mukaminsa ko kuma su fuskanci tsauraran takunkumi.

Da suke mayar da martani, shugabannin sojoji a Nijar sun yi gargadi kan duk wani matakin soji a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar ta Nijar.