On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Sojojin Gabon Sun Sanar Da Juyin Mulki

Sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon tare da sanar da  karbi mulki.

Sun ce sun soke sakamakon zaben da ka gudanar  ranar Asabar, inda aka ayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce Mr Bongo ya samu nasara ne da kasa da kashi biyu bisa uku na kuri'un da aka kada a zaben da 'yan adawa suka ce an tafka magudi.

Hambarar da shi zai kawo karshen mulkin shekaru 53 da iyalan gidansu ke yi  a Gabon.

Sojoji 12 ne suka bayyana a gidan talabijin dake sanar da soke sakamakon zaben tare da rusa dukkan hukumomin kasar.

Daya daga cikin sojojin ya fada a tashar talabijin ta Gabon 24 cewa, "Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu."

Mr Bongo ya hau karagar mulki lokacin da mahaifinsa Omar ya rasu a shekara ta 2009.