On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Sojoji Sun Kara Kubutar Da Wata Dalibar Makarantar Chibok Bayan Shafe Shekara Tara A Hannun Boko Haram

CHIBOK

Dakarun sojin kasar nan sun samu nasarar kubutar kubutar wata Dalibar makarantar Chibok ma shekara 27, mai suna Mary Nkeki, Bayan shafe shekara Tara da Sace ta.

An gabatar da  Dalibar  ne  a shalkwatar  Bataliyar  soji masu gudanar da shirin sumame na Operation Hadin kai dake Maiduguri a jihar Borno a  jiya.

Kasancewar ta Hamsin da Biyar daga cikin jerin  ‘yan matan da aka sace,  Mary Nkeki  ta baiyana cewar Mijinta  wanda  ya kasance  dan Boko Haram mai suna Adam, Shi  ne  ya yi kokarin ganin ta kubuta, sakamakon mika  wuya ga dakarun sojin kasar nan  da  ya yi.

Ta baiyana cewar ta haifi yara biyu tare da shi, Sai dai dukkaninsu sun  rasu,  Ta kuma baiyana cewar akwai  soyayya  tsakaninta da Mijin nata, Kuma  tana fatan  sun  sake  haduwa da shi domin dorawa daga inda suka tsaya.