On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Sojoji Sun Halaka Mayakan ISWAP Kimanin 100

Rundunar sojin saman kasar nan ta baiyana cewar dakarunta masu gudanar da shirin sumame na Hadin Kai da Hadarin Daji sun samu nasarar halaka mayakan ISWAP da sauran mayakan tada kayar baya kimanin 100, a luguden wuta ta sama da ta yi masu.

 

Wata sanarwa da kakakin rundunar  Edward  Gabkwet  ya  fitar, Ya ce  da  safiyar  ranar Asabar din data gabata, Dakarun suka  farwa sabbin maboyar  ‘yan tada kayar bayan dake  Bukar  Merama  kusa da tabkin Chadi a jihar Borno.

Ya kara da cewar  Luguden wutar ta sama ya  zama  wajibi  biyo bayan yadda  yan tada kayar  bayan suka mayar  da  yankunan Suwa  zuwa  Bukar  Meram, maboyarsu  da suke shirya kai hare-hare.