On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Shugabar Matan Jam'iyyar PDP Ta Kasa Ta Mutu

Jam’iyyar PDP ta sanar da mutuwar shugabar matan jam’iyyar ta kasa Farfesa Stella Effah Attoe.

Marigayiyar  ta kasance  wakiliya  a cikin kwamitin gudanarwar  jam’iyyar  na kasa, inda  ta mutu a jiya  lahadi, kamar yadda iyalanta suka tabbatar  bayan  tayi fama da gajeriyar jinya.

Sanarwar da sakataren yada labaran jam’iyyar  na kasa Debo Olugunagba  ya  fitar,  Ya baiyanar rasuwar  farfesa stella a matsayin wani babban wagegen gibi  ga kasar nan.

Shima  dan takarar  shugaban kasa  a zaben da  ya gabata karkashin jam’iyayr  PDP, Atiku Abubakar ya baiyana kaduwarsa  da  mutuwar  marigayin tare da baiyanata  a matsayin gwarzuwar  dake wakiltar  mata  ta kowane bangare.