Anyi wani abu mai kama da wasan kwaikwayo a ranar Talata lokacin da shuwagabannin kananan hukumomin jihar Ogun suka durkusa suka roki gwamna Dapo Abiodun da ya yafe musu kan takardar koke akansa da daya daga cikinsu ya rubuta.
Shugaban karamar hukumar Ijebu ta Gabas, Wale Adedayo, ya zargi gwamnan da rike kason kananan hukumomin da asusun muhalli da sauran hakkokinsu na tsawon shekaru biyu.
Shugaban karamar hukumar wanda kuma dan jam’iyyar APC ne, ya roki hukumar EFCC da ICPC da su binciki gwamnan domin samun hakokinsu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa na alif 1999 ya tanada.
Sai dai gwamnan a wata sanarwa da ya fitar ya ce bai taba yin katsalandan a kudaden kananan hukumomi ba, yana mai cewa akwai kwamitin hadin gwiwa da Jami’an kasafta arzikin kasa dake kula da kudaden kananan hukumomin.
Sai dai kuma a wani yanayi na janye zarge-zargen, shugabannin kananan hukumomin da suka hada da shi kansa Adedayo, sun mamaye ofishin gwamnan, inda suka durkusa tare da rokon gafara.