Shugaban kungiyar Al’ummar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, Farfesa Geroge Obiazor ya mutu, Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma ne ya tabbatar da mutuwar tasa ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram a daren jiya.
Ya baiyana mutuwar jagoran Igbon kuma tsohon jakadan kasar nan a Amurika, da kasar Banu Isra’ila a matsayin babban rashi ga al’umma jihar Imo da shiyyar kudu maso gabashin kasar nan da kuma kafatanin Najeriya.
Gwamnan jihar Imo ya baiyana cewa, Iyalansa zasu sananar da lokacin da za’a yi bikin binne marigayin, Dama tun da sanyin safiyar ranar Laraba ne, aka fara yada jita-jitar mutuwar shugaban kungiyar Kabilar Igbon.