Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya dakatar da yakin neman zabe bayan wata rashin lafiya da ya kamu da ita a lokacin da ake wata hira da shi kai tsaye a gidan talabijin inda aka dakatar da gabatar da hirar ba zato ba tsammani.
Bayan hutun mintuna 20, Shugaban kasar ya sake dawo wa hirar inda ya baiyanawa jama’a cewar yana fama da ciwon ciki mai tsanani.
Erdogan mai shekaru 69, na fuskantar yakin neman zabe mafi zafi a kasar, yayin da aka zabi babban madugun adawa Kemal Kilicdaroglu domin ya tsayawa takara a rukunin wasu jam'iyyun siyasa shida inda zai kara da shugaban kasar.
Sai dai kuma jagoran yan hamaiyyar na daga cikin jiga-jigan 'yan adawa da suka yi wa shugaban fatan samun sauki cikin gaggawa.