Shugaban Kasar Burundi Evariste Ndayishimiye ya sauke Firiyiministan kasar tare da wani babban hadiminsa daga kan kujerunsu a yau Laraba, bayan wani gargadi na yunkurin yi masa juyin mulki da aka yi.
Ya sauke firiyiministan mai suna Alain Guillaume Bunyoni da kuma shugaban fadar gwamnatinsa Janaral Gabruek Nizigama.
A wani taron gaggawa da Majalisar ministocin kasar ta kirawo, ta amince da nada Ministan tsaro na aksar Gevais Ndirakobuca a matsayin wanda zai maye gurbin firiyiministan bayan da aka kada masa kuri’a 113.