Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, Ya baiyana cewa, ana saran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kudirin kasafin kudin badi a gaban zauren majalisar dokokin ta kasa, a farkon makon watan Oktoban bana.
Kakakin majalisar ya baiyana haka ne lokacin da yake yiwa manema Labarai jawabi, jim kadan bayan kammala duba dakunan taron sauraron ra’ayoyin jama’a na 28 da kuma 234 da majalisar zata yi amfani dasu a matsayin na wucin gadi wajen rika gudanar da zamanta na yau da kullum, a sakamakon gyare-gyaren da ake kan yiwa zaurin majilar wakilan a halin yanzu.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na Jagorantar taron Majalisar Zartawa na kasa
Yace za’a kammala saita wurin da majalisar zata rika amfani dashi a matsayin zauren ta na wucin gadi gabanin ranar 20 ga watan da muke ciki, lokacin da majalisar zata koma bakin aiki.
Femi Gbajabiamila ya kara da cewa, aikin gyara majalisar zai fi amfanar sabbin yan majalisa masu zuwa kasancewar ba zai kammala ba har cikin watan Augustan badi.