Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ya bukaci al'ummar kasar nan dasu bashi kwanaki Bakwai domin kawo karshen matsalolin kudi da al'ummar kasa suke a ciki, biyo bayan sauyin takardun kudi na naira da babban bankin kasa ya bullo dashi.
Shugaban kasar na wannan kalaman ne a yayin da kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC suka kai masa ziyara a fadarsa dake Villa, inda suka baiyana cewa yanayi da ake ciki na zama babbar barazana ga nasarorin da gwamnati mai ci ta samu a bangaren daga likafar fannin tattalin arzikin kasa.
Sai dai shugaban kasar ya baiyana cewa sauya fasalin takardun kudin da aka yi zai samar da cigaba ga bangaren tattalin arzikin kasa, yana mai baiyana shakkunsa kan yadda Bankuna ke nuna kokontonsu wajen samun nasarar shirin.
Ya kara da cewa wasu bankunan sun damu ne kawai da kansu , kuma koda an kara masu shekara daya , ba za'a samu magancewar matsalar ba, saboda son zuciyarsu.
Kazalika shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya kallin halin da al'umma suke ciki dangane da karancin kudin naira ta Akwatin Talabijin, kuma kwanaki goma da aka kara zai magance tsananin da al'ummar suke dashi.