shugaban kasa Bola Tinubu ya karbi bakuncin tawagar jagororin malaman addinin musulunci na kasar nann karkashin jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi, domin basu damar shiga tsakani kan rikicin da ya kunno kai a kasar Nijar.
Jagororin sun je fadar shugaban kasar ne domin tattaunawa da shi kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar.
Idan dai za a iya tunawa a ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasar ya bayyana cewa, har yanzu ana kan cigaba da tattaunawa domin ganin an shawo kan rikicin siyasar Nijar cikin ruwan sanyi.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Shugaban kungiyar Izala ta kasa, Sheikh Bala Lau, ya ce tawagar ta yi alkawarin samar da mafita mai dorewa a makwabciyar kasar Nijar.