Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta kasa NCAA, Kyaftin Musa Shuaibu Nuhu, ba tare da bata lokaci ba
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar, ta ce dakatarwar ita ce zata baiwa hukumar EFCC damar gudanar da bincike kan ayyukan shugaban hukumar da aka dakatar da sauran manyan jami’an hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa NCAA.
Shugaban ya umurci Kyaftin Chris Najomo da ya fara aiki a matsayin mukaddashin shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta kasa a nan take.
Shugaban ya kuma umurci Ministan Sufurin Jiragen Sama da ya fara shirin daukar Shugaban Jami’ar da sauran manyan jami’an gudanarwa na Jami’ar koyar da harkokin Sufurin Jiragen Sama ta Afrika da aka samar a nan Najeriya.
Bugu da kari shugaban kasar ya sauke wasu shugabanni da kuma daraktoci guda shida dake hukumomi daban daban na ma’aikatar sufurin jiragen sama ta kasa, tare da maye gurbinsu da wasu.