To manyan zabukan kasar nan dai sunzo kuma sun tafi, Sai dai kuma har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari na cigaba da taba alli kan babban dalilin da yasa manyan jam’iyyun hamaiyya suka sha kaye a zaben.
A cewarsa a yayin da jam’iyyar APC ta dage domin ganin ta rike kujerar shugaban kasa,Su kuwa jam’iyyun hamaiyya sun dogara ne da shacin fadin da ake na cewar jam’iyya mai mulki ba zata ci zabe ba, wanda hakan suka sakankance.
Shugaban kasar ya baiyana haka a jiya,Yayin ganawarsa da gwamnonin jam’iyyar APC a fadarsa dake Abuja, Ya ce jam’iyyarsa ta APC ta zage damtse inda ta yi ba dare ba rana tare kuma da yin taka tsan-tsan domin ganin ta samu nasara a zaben.
Kazalika shugaban kasar ya jaddada cewar manyan jam’iyyun hamaiyya sunsha kaye a zaben shugaban kasar nan, saboda wuce makadi da rawa, Sannan kuma ya kalubalance su kan yadda suka ki amincewa da shan kaye.