Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su Kasance masu yakini da karfin da sojojin kasar nan ke da shi wajen kare Najeriya da kuma samar da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
A cikin wata sanarwa da Hadimin shugaban kasa ta bangaren yada Labarai Femi Adesina, ya fitar, shugaban kasar ya baiyana haka ne, yayin da yake bude gasar sojojin ruwa ta kasa karo na 12 ta shekarar bana a Legas a ranar Alhamis, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa sojojin za su ci gaba da gudanar da aikinsu na domin dakile matsalolin rashin tsaro da sauran kalubale da kasar nan ke fuskanta.
SHUGABAN KASA BUHARI
Shi ma da yake nasa jawabin, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bayyana rundunar sojojin ruwan kasar nan a matsayin wata abokiyar huldar ‘yan sandan jihar Legas wajen tsaron rayuka da kuma kare dukiyoyi.
Kazalika shima babban Hafsan sojin ruwa na Kasa, Vice Admiral Awwal Gambo, Ya yi alkawarin cewa rundunar sojin ruwa za ta ci gaba da yaki da satar danyen mai da sauran laifukan fashin teku tare da tabbatar da cewa kasar nan ta fice daga jerin kasashen da ke fama da matsalar fashin teku.