A yaune Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron kolin shugabannin kasashen Tekun Guinea a birnin Accra na kasar Ghana.
Hadimin shugaban kasar ta fuskar yada labarai,Femi Adesina ne ya tabbatar da haka a Abuja, Y ace shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo ne zai jagoranci taron.
Ya kara da cewar shugaban kasar na daga cikin manyan masu gabatar da jawabi a wajen taron,wanda za’a tattauna kan dabarun inganta tsaro da samar da zaman lafiya da kuma yaki da ‘yan fashin teku.