Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron shugabannin kungiyar Kasashen Renon Ingila da ke gudana a ‘kasar Rwanda daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Yunin da muke ciki.
Wata sanarwa da fadar shugaban Kasa ta fitar a yau Laraba ta ce shugaban zai halarci bude bikin a hukumance wanda za’a gudanar ranar juma’a.
Taron mai lakabin CHOGM 2022, zai Taba Alli kan halin rayuwa da kuma ci gaban al'ummar ‘kungiyar fiye da biliyan biyu da ke zaune a ‘kasashe 54 na nahiyoyin Afirka da Asiya da Amurka da Turai da kuma yankin Pacific.
Ministci da manyan jami'an gwamnatin Taraiyya takwas ne za su yi wa Buhari rakiya zuwa Rwanda.
Ana sa ran shugaban zai dawo Najeriya ranar Lahadi, 26 ga watan Yunin da muke ciki.