On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Shugaban Kasa Buhari Yayi Tir Da Kisan Gillar Da Aka Yiwa Wani Fasto A Kaduna

SHUGABAN KASA BUHARI

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi All..h wadai da kisan gillar da aka yi wa wani limamin majami’ar mabiyar darikar Katolika, Rev. Fr. John Cheitnum dake Kafanchan, kwanaki hudu bayan wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shi.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya fitar a ranar Laraba, Shugaba  Buhari ya ce ya damu matuka da kisan gillar da wasu  batagarin mutane suka yi wa faston, wanda ga bisa alamu sunyi haka ne domin haifar da rudani a kasa.

A cewar shugaban kasa, tsaron dukkan ‘yan Nijeriya shi ne babban abin da ya sa a gaba.Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da shugabannin kungiyar Kiristoci ta Najeriya a Jihar Kaduna bisa rasuwar limamin majami’ar.