Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce duk da kasancewar ’yan Najeriya kabilu daban daban da kuma mabanbanta al’adu sun hade kansu wuri guda inda suke cin cin gajiyar ‘yancin fadin albarkacin baki batare da wata tsangwama ba.
Ya ce duk da zazzafar suka da ake samu a siyasance gabanin zaben shekara mai zuwa, Yan Najeriya sun hada kai ta hanyoyi da yawa fiye da rabuwar kawunan da ake samu a baya.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar wasikun kama aiki daga jakadu da sauran jami’an diplomasiyya na wadansu kasashe shida a fadar sa da ke Abuja.
Jakadun sun hada dana Indiya, Mista Gangadharan Balasubramanian sai Jamus, Mrs Annett Gunther da kasar Sudan, Mohamed Abdelmannan sai jakadiyar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, uwargida Gerengbo Pascaline da jakadan Kasar Falasdinu, Abdullah Shawesh da kuma jakadan kasar Netherlands, Mr Willem Plomp.