Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga birnin Madina zuwa birnin Makkah na kasar Saudiyya, a ci gaba da ziyarar aiki ta kwanaki takwas da ya ke yi a kasa mai tsarki.
A lokacin da yake birnin Madina, shugaban kasar ya ziyarci wuraren tarihi na addini da suka hada da wani babban wajen bikin baje koli na kasa da kasa na kayayyakin tarihin Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wasalam.
Ya kuma yi salloli biyar da kuma sallar tarawihi a masallacin Annabi dake birnin Madina kafin ya tashi zuwa Makkah daren jiya Laraba.
Ana sa ran shugaban kasa zai yi gabatar da ibadar umarah da zarar ya sauka birnin na Makkah a daren jiya.