Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin hakar rijiyar mai a karamar hukumar Obi ta jihar Nasaraw
Da yake jawabi jim kadan bayan kaddamar da aikin ta hanyar allon gani gaka a ranar Talata, Shugaba Buhari ya baiyana fatan cewar sabon aikin zai temaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da inganta rayuwar daukacin ‘yan Najeriya.
Kazalika ya yi kira ga kanfanin sarrafa albarkatun mai na kasa da ya tabbatar da cewar aikin hakar rijiyar danyen mai bai haifar da wasu matsaloli ga yankunan da suke wajen ba.
Shima a nasa bangaren, karamin ministan albarkatun mai na kasa,Timpre Sylva, ya ce aikin hakar rijiyar man zai temaka wajen samar da arziki ga jama’ar jihar Nasarawa da kuma kasa baki daya.