A jiya ne taron majalisar zartarwa na kasa ya amince da kudurin kasafin kudin shekara mai zuwa na kimanin naira tiriliyan 27 da bilyan 5, wanda hakan ya nuna an samu karin sama da Tiriliyan 1 daga ainihin naira Tiriliyan 26 da digo 1, da aka yi tsammanin za’a dora kasafin kudin mai zuwa.
Ministan kasafi da kuma tsare-tsaren tattalin arzikin kasa, Abubakar Bagudu ne ya sanar da amincewar ga manema Labarai na fadar shugaban kasa, jim kadan bayan kammala zaman da aka yi.
Ya ce gwamnatin tarayya na hasashen samun naira tiriliyan 18 daga bangaren biyan haraji a kakar kudi ta shekara mai zuwa, Inda ya yi alkawarin yin cikakken jawabi akan kudirin kasafin kudin, da zarar shugaban kasa ya gabatar da shi a gaban hadakar zaurikan majalisun dokokin kasa.
A nan kuma matukar ba wani sauyi aka samu ba, Ana saran shugaban kasa Bola Tinubu, zai gabatar da kudirin kasafin kudin shekara mai zuwa a gaban hadakar zaurikan majalisun kasa a gobe Laraba.
Wannan ne karon farko da shugaban kasar zai gabatar da kasafin kudi na kimanin sama da naira tiriliyan 27 a gaban ‘yan majalisun dokokin kasa tare da yi masu jawabi.
An samar da matakan tsaro gabanin gabatar da kasafin kudin da za’a yi.
A wani bangaren kuma, Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sake nada Malam Mele Kyari a matsayin shugaban Kanfanin mai na kasa , Kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ya fitar a jiya.