Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Dr. Iyorchia Ayu ya mika ragamar tafiyar da jam’iyyar ga matimakinsa na shiyyar Arewa Umar Iliya Damagun.
Mashawarcinsa ta bangaren yada labarai da sadarwa, Simon Imobo Tswam ne ya baiyana haka da maraicen ranar Talata, inda ya baiyana cewa shugaban jam’iyyar zai yi balaguro zuwa ketare har zuwa karshen watan da muke ciki.
Babu dai wasu dalilai da aka baiyana kan balaguron da shugaban jam’iyyar zai yi zuwa ketare, duk da rikicin cikin gida da jam’iyyar ke fama dashi, Ana saran jam’iyyar ta PDP zata kaddamar da yakin neman zabenta a ranar 28 ga watan satumbar da muke ciki.
Shugaban jam'iyyar PDP da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas
Hakan na nufin cewa Sanata Iyorchia Ayu zai kasance baya gida Najeriya a lokacin da jam’iyyar zata kaddamar da kwamitin yakin neman zabenta na kasa gabanin babban zaben shekara mai zuwa.