Magatakardan Hukumar Shirya jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta kasa, Farfesa Ishaq Oloyede, Ya baiyana matakin tafiya yajin aiki da Kungiyar Malaman jami’oi ta kasa ASUU ta dauka, a matsayin abunda bai zama wajibi ba.
Oloyede ya baiyana haka ne lokacin da yake gabatar da wasu kayayyaki na mIlyoyin Naira ga Asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin domin inganta harkokin lafiya, Wanda Hukumar ta samar hadin gwiwa da kasar Amurika.
A cewarsa yawan tafiya yajin aiki da Manyan Makarantun kasar nan keyi shine babban abunda ya kara illata Dalibai da kuma kasa Baki Daya.
Sauran Cibiyoyin kiwon Lafiyar da suka amfana daga tallafin, sun hada da Asibitin koyarwa na Maiduguri da Asibitin koyarwa na jami’ar Yusuf Maitama Sule dake nan Kano, da kuma wasu Asibitoci 9 dake shiyyoyi 6 na kasar nan.